James 3

1Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, ‘yan’uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani. 2Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa.

3Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya. 4Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so.

5Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta. 6Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al’amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi.

7Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma. 8Amma game da harshe, babu wani a cikin ‘yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa.

9Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la’antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah. 10Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la’antarwa. ‘Yan’uwana, ai, wannan bai kamata ba.

11Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya? 12‘‘Yan’uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba.

13Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali’u da hikima ke sawa. 14Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya.

15Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu. 16Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta. 17Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma. Kuma ‘ya’yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.

18

Copyright information for HauULB